✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Buhari ya sa a raba wa ’yan Najeriya hatsi metric ton 40,000

Za a bi tsarin rabon tallafin COVID-19 wajen rabon hatsin ga jama'ar Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a fito da hatsi da yawansa ya kai metric ton dubu arba’in daga rumbunanta a raba wa ’yan Najeriya domin kawo saukin tsadar kayan abincin da ya addabi  kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin da nufin rage radadin tsadar kayan abinci musamman a watan Ramadan da ake ciki da kuma lokacin bukukuwan Sallah da na Ista suke kara matsowa.

“Zai rage matsalar tsadar kayan abinci da ake fama da ita kasar nan sannan ya kawo wadatuwar hatsi a kan farashi mai sauki domin mutane su samu yin azumin watan Ramadan da kuma bukuwan Ista da na Sallah cikin sauki.

“Daga cikin hatsin akwai kason da za mu ba wa Ma’aikatan Agaji da Ayyukan Jin Kai, ta raba wa jama’a,” a cewar Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara, Mohammed Abubakar.

Da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata, ministan ya ce tuni aka kammala aikin fara rabon hatsin ga ’yan Najeriya bisa tsarin da aka yi rabon metric ton 70,000 na hatsin da gwamnatin ta fitar a lokacin kullen COVID-19 a fadin kasar.

Ministan, wanda Shugaba Buhari ya gayyata domin jin bahasin halin da ake ciki daga bakinsa, ya bayyana cewa Ma’aikatan Agaji da Ayyukan Jin Kai, za ta samu Metric ton dubu goma sha biyu daga cikin metric ton 40,000 da za a fito da shi daga rumbun hatsin gwamnati domin raba wa ’yan Najeriya masu karamin.

Ministan ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aikin rabon hatsin a bisa umarnin shugaban kasa.