✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Akeredolu murnar lashe zaben Ondo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Rotimi Akeredolu murnar lashe zabe.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Rotimi Akeredolu murnar lashe zabe a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa’adi na biyu.

Shugaban kasar ya taya Mista Akeredolu murna cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta bakin mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina.

A yau Lahadi ne dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Abel Idowu Olayinka, wanda shi ne Babban Bature zabe na INEC, yayin bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi ya ce Akeredolu ya samu nasara ne da kuri’a 292,830.

Alkaluman sun nuna Akeredolu da ke neman wa’adin mulki na biyu a jam’iyyar APC ya samu gagarumar rinjaye a 15 daga cikin Kananan Hukumomi 18 na jihar.

Babban abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jami’ar PDP ya samu kuri’a 195,791 a matsayi na biyu a zaben.

Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar ZLP shi ne ya zo na uku bayan ya samu kuri’a 69,127.