✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Amurka murnar cika shekara 245 da samun ’yanci

Ina fatan huldar Najeriya da Amurka za ta ci gaba bunkasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya takwaransa Shugaba Joe Biden, gwamnati da kuma al’ummar Kasar Amurka murnar bikin cika shekar 245 da samun ’yanci kai.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ta bayyana alfahari kan yadda gwamnatin Shugaba Biden ke kokarin magance kalubalen da Amurka ke fuskanta.

Daga cikin manyan kalubalen da Amurka ke fuskanta kamar yadda sanarwar ta zayyana akwai nuna wariyar launin fata da kuma yaki da annobar cutar Coronavirus, daya daga cikin kasashen duniya da annobar ta fi munana.

Shugaba Buhari ya bayyana farin ciki kan yadda gwamnatin Shugaba Biden ke kokarin inganta alakar Amurka da kasashen Afirka domin tabbatar da ci gaban nahiyyar.

Kazalika, Buhari ya bayyana cewa bisa la’akari da tsarin dabbaka dimokuradiyya da kuma kiyaye dokoki da kasashen biyun suka rika, yana fatan huldar Najeriya da Amurka za ta ci gaba bunkasa domin amfanin al’ummomin kasashen biyu.