✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya taya Lula da Silva murnar lashe zaben shugabancin Brazil

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya shiga sahun takwarorinsa na duniya wajen mika sakon taya murna ga sabon zababben Shugaban Kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya shiga sahun takwarorinsa na duniya wajen mika sakon taya murna ga sabon zababben Shugaban Kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva kan lashe zabensa.

Sakon taya murnar na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar, a ranar Litinin a Abuja.

Buhari ya ce yana fata nasarar da Lula ya samu za ta kara dankon zumuncin da ke tsakanin Najeriya da Brazil.

“Ina fatan za mu yi aiki tare da sabon zababben Shugaban Kasar Brazil domin ci gaba da karfafa dakon zumuncin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu,” in ji Buhari.

Luiz, wanda tsohon Shugaban Kasar ne ya samu nasarar lashe zaben na yanzu ne bayan da ya fito daga gidan yari.

Ya dai lashe zaben ne bayan ya kayar da Shugaban Kasar mai ci, Jair Bolsonaro, a zaben da aka gudanar a karshen makon nan.

(NAN)