✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan jajirtaccen mutum ne, inji Buhari

Shugaba Buhari ya yaba kyawawan dabi'un Jonathan a matsayin Shugaba da kuma wakili

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba da jajircewar Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da kuma yadda ya jawo wa Najeriya martaba da kima a idon duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a sakon taya murnar cika shekara 63 a duniya da ya aike wa Mista Jonathan din.

“Shugaba Buhari ya jinjina daukaka mai ban mamaki wadda ba kasafai akan ga irinta ba a fagen siyasar Najeriya da tsohon shugaban kasar ya samu, da kuma jajircewarsa wadda ta ba shi damar aiki a baya-bayan nan a matsayin manzon kungiyar ECOWAS na musamman wajen dawo da zaman lafiya a Jamhuriyar Mali”, inji sakon mai dauke da sa-hannun Hadimin Shugaban Kasa kan Watsa Labarai, Femi Adesina.

A ranar Juma’a ne Mista Jonathan, wanda Buhari ya gada a mulki a 2015. ke cika she 63 da haihuwa.

Ya yi addu’a Allah Ya ba wa tsohon shugaban karin hikima, da lafiya da tsawon kwana mai albarka domin ci gaba da hidimta wa al’umma.