✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Okorocha murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, murnar zagoyowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekaru 58 a duniya. Sakon…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, murnar zagoyowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekaru 58 a duniya.

Sakon taya murnar ya zo ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari ya kuma taya dukkanin makusanta da abokanan huldar Sanata Okorocha, mai wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa murna.

Buhari ya jinjina wa tsohon gwamnan dangane da kyakkyawar akidarsa ta rashin nuna kabilanci a tsakanin al’ummar Najeriya tare da yaba masa a kan Gidauniyar Rochas Okorocha da ya assasa domin tallafa wa mabukata da marasa galihu.

Sanata Rochas ya cika shekara 58 da haihuwa a ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2020.

An haife shi a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar 1962, shekara biyu bayan Najeriya ta samu ’yancin kai.