✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya William Ruto murnar lashe Zaben Kenya

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya William Ruto murnar lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a Kenya. Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun…

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya William Ruto murnar lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a Kenya.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinsa Femi Adesina, Buhari ya yaba wa al’ummar Kenya bisa yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Sanarwar ta ce wannan ya sake nuna cewa tsarin dimokuradiyya, dabi’u da ka’idoji sun kasance hanya mafi kyau da jama’a za su zabi shugabanninsu da kuma dora su a kan su.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya na mutunta kasar Kenya a matsayin babbar abokiyar kawance wajen yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, wanda dogon tarihi na abotar tattalin arziki da cinikayya, da hadin gwiwa mai inganci da kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar Tarayyar Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashe masu tasowa.

Tun farko dai, Shugaban Hukumar Zabe na kasar Kenya ya bayyana Mataimakin Shugaban Kasar William Ruto, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai tsauri – amma wasu jami’an zabe hudu sun yi watsi da sakamakon, lamarin da ya haifar da shakku da rudani kan sakamakon.

A ranar Litinin Shugaban Hukumar Zaben Kenya, ya ce Ruto ne ya lashe zaben zagayen farko da kashi 50.49 na kuri’un da aka kada, wanda ke gaban tsohon Firaminista Raila Odinga da kashi 1.5 cikin dari.

Sai dai ‘yan mintuna kafin Wafula Chebukati ya sanar da sakamakon, Mataimakin Shugabar Hukumar Zaben, Juliana Cherea ta ce ita da wasu kwamishinonin uku “ba su amince da sakamakon zaben ba.”

Kamfanin Dillancin Labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, kakakin babban abokin hamayyar Ruto, Raila Odinga, ya yi watsi da sanarwar da Shugaban Hukumar Zaben ya yi a matsayin Ruto ne ya yi nasara.

A duk lokacin da ake gudanar da tantancewar da aka fara a ranar Laraba, an yi ta zargin magudin zabe da kuma yadda jami’an zabe ke tafka magudi, musamman daga bangaren Odinga.

A yayin da ake fargabar cewa zarge-zargen magudin zabe na iya haifar da zubar da jini kamar yadda ya faru a zaben 2007 da 2017, tuni Cherea ta bukaci bangarorin da su warware duk wata takaddama a kotu.