✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban ’yan sanda

An kara masa wa'adi kwana uku bayan ranar da ya kamata ya yi ritaya daga aiki.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara wa Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Mohammed wa’adin aikinsa da wata uku.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi ya sanar da sanar da haka ne a ranar Alhamis, kwana uku bayan cikar wa’adin Shugaban ’yan sandan.

Ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da ’yan jarida Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ya ce an kara wa Mohammed Adamu lokacin ne domin a samu isasshiyar damar zabar magajinsa.