✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya umarci a fatattaki ’yan bindiga daga hanyar Kaduna zuwa Abuja

Buhari ya ce ’yan Najeriya sun cancanci su zauna lafiya cikin aminci.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hukumomi tsaro da suka kawo karshen barazanar ’yan bindiga a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma sauran sassa a kasar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ra’uf Argebesola ne ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Tsaro da Shugaba Buhari ya jagoranta ranar Alhamis a Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasar, Ministan ya ce Shugaba Buhari ya umarci dakarun tsaro da sauran hukumomin tsaro ciki har da kungiyoyin leke asiri, a kan kada su yi kasa a gwiwa a ci gaban da ake samu na kawo karshen ta’addanci.

A cewarsa, shugaba Buhari ya umarci dukkanin jami’an tsaro na kasar da su kara zage dantse domin ganin an magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar kama daga ta’addancin ’yan daban daji da masu satar mutane da neman kudin fansa.

A yayin da shugaban kasar ke tunatar da jami’an tsaron cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da batun kakkabe ababen da ke tayar da zaune a kasar, ya kuma ankarar da su a kan cewa ’yan Najeriya sun cancanci su zauna lafiya cikin aminci.

Kazalika, shugaban kasar ya ba da umarnin jibge karin jami’an tsaro domin su kara tsananta sintiri a kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa Abuja la’akari da yadda sahu a yanzu ba zai dauke ba saboda gabatowar karshen shekara kasancewarsa lokacin da a aka saba gudanar da shagulgulan bikin Kirsimite da na sabuwar shekara.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan umarni na shugaban kasar na zuwa ne kwanaki bayan da ’yan bindiga suka kai wani mummunan hari a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka kashe wani tsohon dan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Sagiru Hamidu sannan suka yi awon gaba da mutane da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.