✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ware biliyan N13.3 domin tsaron al’ummomi

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 13.3 domin kaddamar shirin samar da tsaro a cikin al’ummomi a fadin kasa. Matakin na daga…

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 13.3 domin kaddamar shirin samar da tsaro a cikin al’ummomi a fadin kasa.

Matakin na daga cikin yunkurin taimaka wa magance matsalar tsaro da ke addabar yankunan kasar.

Hakan na daga cikin matsayar da taron Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa ya cimma a ranar Alhamis, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.

Taron karo na shida ya karbi rahoton Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti a kan shirin samar da tsaro da kuma sanya ido a cikin al’ummomi, wanda ya jaddada muhimmanci hada kai da masu ruwa da tsaki domin cimma manufar.

Majalisar Tattalin Arzikin Kasar ta umarce shi ya yi aiki tare da wasu gwamnoni biyu su hada kai da Ministar Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Suleiman Adamu da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha kan yadda za a sarrafa kudaden aiwatar da shirin

Ta bukaci kwamitin gwamnonin da ministocin da ya kawo mata rahoto da shawarwarin, sannan ya rika ganawa jefi-jefi gwargwadon bukata, domin sanar da ita irin nasarorin da ake samu wajen magance matsalolin tsaro da miyagun laifuka.