✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi alhinin mutuwar Janar Domkat Bali

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Gwamnati da kuma daukacin al’ummar jihar Filato ta’aziyyar mutuwar Tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Domkat Yah Bali, wanda ajali…

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Gwamnati da kuma daukacin al’ummar jihar Filato ta’aziyyar mutuwar Tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Domkat Yah Bali, wanda ajali ya katse masa hanzari a ranar Juma’a.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ta ce Buhari wanda ya yi magana da matar marigayin, Esther, ya jajanta wa ’yan uwa da makusanta dangane da wannan rashi.

Sanarwar ta ce akida ta kishin kasa da Janar Bali ya rika a rayuwarsa ta aiki soja za ta ci gaba da karfafa gwiwar sojoji masu taso wa sannan za a ci gaba da tuna wa da irin shugabancin da ya gudanar wajen hidimta wa kasar nan a fannoni daban-daban.

Shugaban kasar bayan jajanta wa tare da rarrashin ’yan uwan mamaci, ya kuma yi fatan mutuwa ta zama hutu a gare shi.

Aminiya ta ruwaito cewa sanarwa ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya nada wata tawaga karkashin jagorancin Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, domin zuwa ta’aziyya ga iyalan marigayi Bali da kuma gwamnatin jihar Filato dangane da rashin da suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Ministan Tsaron Kasar ya mutu ne a birnin Jos na jihar Filato bayan ya sha fama da rashin lafiya.