✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi alhinin mutuwar ’yar uwar Fayose

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Moji Ladeji, yayar tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose. Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina ya…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Moji Ladeji, yayar tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina ya wallafa ta’aziyar ta shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba.

Shugaban Kasar ya kuma mika ta’aziyyarsa ga dukkanin abokai, makusanta da dangin marigayiya Moji dangane da wannan rashi da suka yi.

Ya nemi da su dauki dangana kasancewar mutuwa tana kan kowa.