✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi alhinin rasuwar Sarkin Kwatarkwashi

Mutuwarsa babban gibi ne da ba za a taba iya cike shi ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin rasuwar Sarkin Kwatarkwashi, Alhaji Ahmad Umar.

Sarki Mai Kwatarkashi shi ne basarake mafi dadewa a kan gadon sarauta a Jihar Zamfara, wanda ya shafe kimanin shekera 61 a matsayin Sarkin garin Kwatarkwashi da ke Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, ta bayyana rasuwar Sarkin a matsayin wawakeken gibi da ba za a taba iya cike shi ba.

Shugaba Buhari, wanda ya misalta marigayin a matsayin mutumin kirki da kulawa da duk wadanda suka rabe shi, ya ce shekaru 61 da marigayin ya yi a kan karagar mulki ya sadaukar da su ne wajen ci gaban al’ummarsa, wanda a dalilin haka ne al’ummar gobe za ta ci gaba da yaba masa.

Buhari ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin, yayin da ya bukaci al’ummar masarautar Kwatarkwashi da Jihar Zamfara baki daya da su jure wannan rashi da suka yi.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi jana’izarsa Mai Kwatarkwashi da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Alhamis a fadarsa da ke garin na Kwatarkwashi.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar III ne dai nada marigayin sarauta a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1961.

Ya rasu yana da shekara 93 a duniya.