✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi alkawarin dawo da martabar Arewa —Matawalle

Matawalle ya roki gwamnoni su ajiye bambancin siyasa a ciyar da Najeriya gaba.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya ce Shugaba  Buhari ya sha alwashin dawo da martabar Arewa da kuma kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da gwamnan ya sanya wa hannu.

  1. Batanci: Za mu bi diddigin shari’ar Abduljabbar har a kammala ta – Ganduje
  2. ’Yan damfara sun dura wa mutum 800 ruwa a matsayin rigakafin COVID-19

“Shugaban Kasa ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro tare da dawo da martabar Arewa.

“Lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen kashe-kashe da zubar da jini, sannan mu koyi halin yafiya da kuma mance abubuwan da suka faru a baya.

“Za mu mai da hankali wajen ciyar da kasa gaba ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba,” a cewar Matawalle.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taron gwamnonin Arewa da aka gudanar don nemo bakin zaren matsalar tsaro.

Ya ce gwamnonin Arewa na kokari matuka wajen tallafa wa Shugaban Kasa don kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Kazalika, Matawalle ya roki masu ruwa da tsaki, masu kudi, ’yan kasuwa da ’yan siyasa da su taimaka wajen dakile matsalolin tsaro tare da kawo cigaba a yankin.

Ya ja hankalin shugabanni kan nemo mafita tare da ciyar da Najeriya gaba.

“Ya kamata shugabanni su kau da bukatar kashin kansu su kawo karshen kashe-kashen rayuka da salwantar da dukiyoyi.

“Matsalar tsaro musamman a yankin Arewa Maso Gabas da kuma hare-haren ’yan bindiga sun kawo nakasu ga tattalin arziki, harkar ilimi da noma a Arewa,” a cewar gwamnan.