✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ganawar sirri da Gwamnan Kano Ganduje

A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni…

A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe.

Duk da dai Shugaban Kasar ya karbi bakuncin Gwamnonin biyu cikin sirri, akwai yiwuwar ganawarsu na da nasaba da sakamakon zaben Gwamnan Jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba.

A yayin zaben, Fasto Osagie Ize-Iyamu, dan takara na jam’iyyar APC, ya sha kasa a hannun Gwamnan jihar mai ci na jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki.

Ana iya tuna cewa, Ganduje shi ne wanda jam’iyyar APC ta nada a matsayin Shugaban Kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Jihar Edo yayin da ta nada takwaransa na Jihar Imo, Hope Uzodinma a matsayin mataimaki.