✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sa labule da tsohon Shugaba Abdulsalami Abubakar

Ganawar an yi ta cikin sirri ta yadda babu wanda ya san abubuwan da aka tattauna.

Shugaban Buhari ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar, a Fadar Gwamnatin da ke Abuja.

Sanarwar ganawar ta fito daga mai taimaka wa shugaban kasa kan Sabbin Kafafen Yada Labarai, Bashir Ahmad @BashirAhmaad.

“Shugaban Kasa @MBuhari ya karbi bakoncin Janar Abdulsalam Abubakar (Mai Ritaya), a Fadar Shugaban Kasa, Abuja”, kamar yadda ya wallafa.

Sai dai babu wanda ya san makasudin ganawar, saboda babu wata sanarwar da aka fitar game da ganawar.

Tsohon shugaban ya dade yana kiraye-kiraye, kan yadda matsalar tsaro ta tabarbare a fadin Najeriya.

A ranar 24 ga Faibrairu, 2021, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa yin sulhu da ’yan bindiga ba it ace hanya mafi dacewa da gwamnatin Najeriya za ta yi ba.

Abdulsalami Abubakar ya yi wannan kira ne bayan garkuwa da daliban makarantar Sakandaren Kagara da ’yan bindiga suka yi a Jihar Neja.

“Yana da kyau jami’an tsaro su hada kai don bullo da sabbin hanyoyin magance matsalar tsaro”.

Janar Abdulsalami, wanda shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, tun a ranar 16 ga watan Fabrairu, ya bayyana yadda gwamnati ta yi sakaci wajen barin rikicin kabilanci ke neman zama barazana a kasa.

“Muna kira ga ’yan kasa da suke cikin damuwa da bacin rai da su ci gaba hakuri.

“Mutane da yawa sun rasa gidajensu. Mun san irin bakar wuyar da manoma ke sha wajen girbe amfani gonarsu.

“Don haka, ya kamata mu hada kai musamman a wannan lokaci da ake shan wahala, mu sanya ido sosai tare da ba wa juna kariya”.