Buhari ya yi ta’aziyyar daliban Nijar | Aminiya

Buhari ya yi ta’aziyyar daliban Nijar

Shugaba Buhari ya jajanta game da rasuwar daliban makarantar firamare da gobara ta ritsa da su a Jamhuriyyar Nijar.

Akalla dalibai 20 ne suka rasa ransu a gobarar ta ranar Juma’a, wadda Buharin ya bayyana kudawarsa da ita.

Sakon ta’aziyyar da ya aike wa Shugaba Mohamed Bazoum, ta ce, “Muna jajanta wa ’yan uwanmu kan wannan iftila’i, tare da tausayawa ga iyalai da dangin wadanda abin ya shafa.

“Wadanda suka rasu ko suka samu rauni kuma muna musu addu’ar samun rahama da sauki.”

Buhari ya yi jajen ne ta bakin mai magani da yawunsa, Garba Shehu.