✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Pelé

Pelé ya rasu a ranar Alhamis yana da shekara 82 bayan ya sha fama da ciwon daji.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya shiga sahun shugabannin kasashen duniya wajen aike da sakon ta’aziyyarsu game da rasuwar fitaccen dan kwallon kafar duniya, Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pelé.

Pelé dai ya rasu me a ranar Alhamis bayan ya sha fama da ciwon daji, yana da shekara 82.

“Ina masa fatan samun rahama. Ya yi rayuwa mai ingaci wajen inganta harkar kwallon kafa da wasanni a fadin duniya.

“Yana da kirki da tsantseni duk da ficen da ya yi a harkar wasanni a duniya.

“Ya rage yadda ake tsangwamar bakaken fata, mabiya addinai da kabilu a harkar wasanni. Pelé ya tafi amma tarihi ba zai manta da shi ba,” in ji Buhari.

Pelé ya lashe Gasar Kofin Duniya har sau uku a rayuwarsa, sannan ya zura kwallaye fiye da 1,280.

Tuni shugabannin kasashen duniya, ’yan kwallo da sauran jama’a suka shiga nuna alhininsu kan rasuwar gwarzon kwallon kafar duniyar.