✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Buhari ya yi tir da kisan ’yan sa-kai a Katsina

Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ’yan sa-kai a dajin Yargoje cikin Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.

A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce harin wanda ’yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar ’yan bangar da dama.

’Yan bindigar sun yi wa ’yan bangar kwanton bauta a dajin a lokacin da suke kokarin kwato wasu shanu da aka sace.

Buhari ya bayyana alhininsa kan rasuwar ’yan bangar tare da jajanta wa iyalansu, yana mai cewa Najeriya ba za ta manta da sadaukarwar da suka yi na kare kasa, tare da yakar miyagun laifuka a kasarsu ba.

“Muna addu’a tare da jajanta wa iyalan mamatan a wannan lokaci na alhini. Muna addu’ar Allah ya gafarta musu,” in ji Buhari.

Aminiya ta ruwaito cewa adadin mutanen da ’yan bindigar suka kashe a kananan hukumomin Bakori da Kankara sun kai 84.

Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari kan Sha’anin Tsaro, Ibrahim Ahmed-Katsina, ya ce gwamnati za ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru domin daukar matakin da ya dace.

Jihar Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin kasar na fama da matsalolin ayyukan ’yan bindiga, wadanda ke yawan kai hare-hare, tare da sace mutane domin neman kudin fansa.