✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa Katsinawa ta’aziyyar kisan mutum 84

Shugaban ya ce sam maharan babu imani a zukatansu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta tare da mika ta’aziyyar shi ga al’ummar Jihar Katsina kisan da ’yan bindiga suka yi wa mutum 84 kwanaki biyu da suka wuce.

A karshen makon da ya gabata ne ’yan bindiga suka kai hari Kananan Hukumomin Bakori da Kankara da ke Jihar, sannan suka kashe mutanen, galibin su ‘yan sa-kai.

Ya bayyana hakan ne yayin taron yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ranar Litinin a Katsina.

Shugaba Buhari ya ce, kisan da ’yan bindigar suka yi ya kara tabbatar da cewa masu irin wannan aiki ba su da tunani ko imani a zukatansu.

Daga nan sai ya kara jaddada kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya baki daya.

Harin ’yan bindigar dai ya biyo bayan kwanton baunar da ’yan bindigar suka yi wa ’yan bangar yayin da suka bi sawun wasu dabbobin da ’yan ta’addan suka sace.

Tun farko sai da Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari ya tura wata tawaga karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muntari Lawal, domin mika ta’aziyyar gwamnatin Jahar Katsina ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a artabun.

Yayin gangamin dai, Bola Tinubu ya bayar da gudunmuwar Naira milyan 100 ga wadanda lamarin hare-hare ’yan bindigar ya shafa a fadin Jihar.