✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa tsaffin ’yan kwallon Najeriya rabon gidaje

Buhari ya cika alkawarin da aka daukar wa ’yan kwallon da suka lashe AFCON 94.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi rabon gidaje ga tawagar ’yan kwallon Najeriya da suka lashe Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta AFCON da aka buga a Tunisia a shekarar 1994.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu wanda ya fidda sanarwar hakan a ranar Alhamis, ya ce wannan wani mataki ne na cika alkawarin da gwamnatin Tarayya ta yi.

Mallam Shehu ya ce za a bai wa kowanensu wadataccen gida mai dakunan kwana uku a duk jihar da suke so a fadin kasar nan kamar yadda wata makala da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya fitar.

Sanarwar ta ce tuni shida daga cikin ’yan tawagar kwallon kafar ciki har da ma’aikatansu sun mallaki nasu gidajen.

Daga cikin wadanda suka samu wannan tagomashi akwai, Peter Rufai, Alloy Agu, Ike Shorounmu, Uche Okechukwu, Samson Siasia, Efan Ekoku, Sunday Oliseh, Benedict Iroha, Isaac Semitoje, Mutui Adepoju, Emmanuel Amukike, Victor Ikpeba, Austin Eguavoen da marigayi Wilfred Agbonavbare.

Sauran sun hada da marigayi Uche Okafor, marigayi Thompson Oliha, marigayi Stephen Keshi, Christian Chukwu, Dokta Akin Amao, Stephen Edema, Kanal A Asielue da B. Aromasodun.