✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba da umarnin fito da jirage don fara sufuri a kamfanin Nigerian Air

Za a fara sufurin ne da jirage guda uku

Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da jiragen sama guda uku domin fara zirga-zirga ka’in da na’in a sabon kamfanin jiragen sama na kasar mai suna Nigerian Air.

Ministan Sufurin Jirgen Sama, Hadi Sirika ne ya bayyana hakan ga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa a ranar Laraba.

Taron dai ya wakana ne karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Fadar Ado Rock da ke Abuja.

Hadi Sirika ya ce za a fara sufurin ne da jirage guda uku kirar kamfanonin Airbus da Boeing, kuma za su fara zirga-zirga ne a iya cikin gida tukunna.

Ministan ya ce daga bisani kamfanin zai fadada sufurinsa zuwa makwabtan kasashe da ma sauran kasashen duniya masu nisa.

Sai dai Hadi Sirika ya ki ya bayyana ranar da jiragen za su fara aiki, inda ya ce komai zai kammala nan ba da jimawa ba.

Tun bayan da aka kaddamar da tambarin kamfanin na Nigeria Air yayin bajekolin jiragen sama a birnin Farnborough da ke ingila a shekarar 2018, fara aikin kamfanin ya ci karo da tarin matsaloli wadanda har sai da suka kai ga dakatar da shi wata biyu bayan bikin kaddamarwar.

Gwamnatin dai ta bayyana daukar matakin a wancan lokacin a matsayin abu mai matukar wahala.

Sai dai Ministan ya ce kofa a bude take ga ’yan Najeriyar da ke da sha’awar sayen hannun jarin kamfanin da su mallaki abin da ya kai kaso 51 cikin 100 don su ma a dama da su a tafiyar da shi.