✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ganawar sirri da TY Danjuma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya yi ganawar sirri da Tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma. Ganawar dai an yi ta ne…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya yi ganawar sirri da Tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma.

Ganawar dai an yi ta ne cikin sirri a fadar shugaban kasa dake Villa a Abuja.

Sai dai ba a bayyana wa manema labarai dalilin ganawar ba, shi ma daga bangarensa TY Danjuma bayan fitowarsa bai bayyana wa manema labarai makasudin ganawar tasa da shugaba Buhari ba.

Ganawar dai ta zo ne kwanaki biyu bayan da shugabannin Kungiyar Dattawa mabiya addinin Kirista na kasa suka bukaci da sake yin gyara dangane da halin da kasar nan ke ciki.

Sai dai ana tunanin ganawar shugaba Buhari da TY Danjuma na da nasaba da halin da kasar nan ta tsinci kanta a ciki, wanda zanga-zangar #EndSARS ta haifar.