✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai gina gidaje 10,000 masu saukin kudi a Kano

Gwamnatin Kano ta ba da fili don gina gidajen a Karamar Hukumar Ungogo.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen gina gidaje 10,000 masu saukin kudi a Jihar Kano, don inganta samar da gidaje ga ’yan Najeriya.

Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA) Sanata Gbenga Ashafa, ya bayyana hakan yayin duba fili mai fadin kadada 500 da Gwamnatin Jihar Kano ta ware don aikin a garin Dawanau na Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar.

Ashafa, wanda Babban Daraktan Ci Gaban Harkokin Kasuwanci na hukumar, AbdulMumin Jibrin ya wakilta ya ce aikin na daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya da nufin magance matsalar karanci gidaje a kasar.

Ya ce Hukumar ta fara shirye-shirye masu inganci na gyara Gidajen Gwamnatin Tarayya a fadin kasar, sannan ta tura ma’aikata zuwa shiyyar Arewa maso Yamma don aiwatar da ayyukan nata da sauri.

Da yake yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje kan filin da ya bayar, Ashafa ya bukaci ma’aikatan Hukumar da su nuna kwarewa da kwazo wurin yin ayyuka masu inganci.