✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Buhari zai kaddamar da aikin Tashar Dala a Kano

Tashar wadda ta kai fadin kadada shida, za a ci gaba da fadada ta idan bukata ta taso.

A ranar Litinin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar Tashar Ruwa ta Tsandauri ta Dala a Jihar Kano.

Babban Daraktan Tashar, Ahmad Rabi’u ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, shirye-shirye sun kammala don kaddamar da sabuwar tashar da ke Zawaciki a Karamar Hukumar Kumbotso.

Rabi’u ya ce tashar ruwan ta kan tudu ta kasa-da-kasa ce kuma irinta ta farko da za ta dinga kwasar kaya daga Kano zuwa sauran sassan duniya.

Ya kara da cewa, duk da tashar ta kai fadin kadada shida, za a ci gaba da fadada ta idan bukatar hakan ta taso.

Rabi’u ya ce dukkanin abubuwan da ’yan kasuwa ke bukata don fitar da kayayyakinsu, da tantancewar Hukumar Kwastam, za a yi shi ne daga Kano.

A nasa bangaren, Shugaban Tashar ta Dala Alhaji Abubakar Bawuo cewa ya yi an samar da tashar ce domin bunkasa kasuwanci a Jihar Kano, kasancewarta cibiyar hada-hadar kasuwanci a Najeriya da ma nahiyyar Afirka baki daya.