✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyara kasar Mali

A karon farko tun bayan dokar kullen annobar Covid-19, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Mali. Buhari za ikai ziyarar ta kwana daya ne…

A karon farko tun bayan dokar kullen annobar Covid-19, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Mali.

Buhari za ikai ziyarar ta kwana daya ne bayan sauraron rahoton da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar masa kan rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar.

A wata kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce Shugaba Buhari zai je kasar ta Mali ce tare da wasu shugabannin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), inda za su hadu a can domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen shawo kan rikicin siyasar kasar.

Sanarwar ta kara da cewa zai kai ziyarar aikin ne a karkashin jagorancin Shugaban ECOWAS, Shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou.

A ranar Talata ce tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Fadar Shugaban Kasar Najeriya tare da rakiyar Mista Jean-Claude Kassi Brou, inda suka bayyana masa halin da ake ciki a kasar Mali, game da rikicin siyasa da kasar ke fuskanta.

Hakan ya sa shugabannin kasashen ECOWAS za su tafi kasar, domin sake tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake cimmawa.

Ana sa ran Shugaban Kasar Mali, wanda shi ne mai masaukin baki Ibrahim Boubacar Keita, da takwaransa na Senegal Machy Sall da Nana Akufo-Addo na Ghana da Alassane Outtara na Cote d’Ivoire za su halarci taron.