✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyara Legas

Tuni jami’an tsaro suka yi wa Jihar Legas tsinke gabanin ziyarar Shugaba Buhari.

Tuni jami’an tsaro suka yi wa Jihar Legas tsinke gabanin ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai jihar a yau Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa, Buhari zai kai ziyara wuni guda jihar ce domin kaddamar da wasu ayyukan gwamnati.

Hakan na kunshe cikin wani sako da hadiminsa na kafofin sadarwar zamani, Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Daga cikin ayyukan da shugaban zai kaddamar, akwai layin dogo a tashar Mobolaji Johnson da ke Ebutte Metta, mai tsawon kilomita 157 wanda zai tashi daga Legas zuwa Ibadan.

Kazalika, shugaba Buhari zai kaddamar da aikin tashar Jiragen Ruwa ta Energy Nature Light Terminal a Tashar Apapa, a wani yunkuri na ci gaba da kaddamar da ayyukan tabbatar da tsaro na sufurin jiragen ruwa da ake kira Deep Blue Project.

Bayanai sun ce tuni tawagar Shugaban karkashin jagorancin Sufeto Janar na ’yan sanda, Usman Baba ta rifa ta isa Legas.