Buhari zai kai ziyarar jaje Zamfara ranar Alhamis | Aminiya

Buhari zai kai ziyarar jaje Zamfara ranar Alhamis

Buhari zai yi tafiya
Buhari zai yi tafiya
    Shehu Umar, Gusau da Sani Ibrahim Paki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai kai ziyara Jihar Zamfara don ya jajanta wa al’ummarta kan yawan hare-haren da ake kai musu.

Gwamnan Jihar ta Zamfara, Bello Matawalle ne ya sanar da hakan a Gusau babban birnin Jihar ranar Talata.

Matawalle ya ce Buhari zai kai ziyarar ne saboda tsananin son da yake yi wa Jihar.

Ya kuma yaba wa Shugaban kan yadda ya ce ya damu da mutanen jihar matuka, lamarin da ya ce shi ne ma babban makasudin ziyarar.

Gwamnan ya ce tuni shirye-shiryen tarbar Shugaban suka yi nisa.