✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai karbo ‘kyautar zaman lafiya’ a Mauritaniya

Shugaban zai karbi kyautar zaman lafiya ne a can

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata mai zuwa zai karbi kyautar “Karfafa zaman lafiya ta Afirka” a birnin Nouakchott na kasar Mauritaniya.

Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce Buharin zai karbi kyautar ce saboda irin rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da kuma yin sulhu a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka.

Kwamitin Zaman Lafiya na Abu Dhabi, ne dai zai gabatar wa Buhari kyautar.

An kafa kwamitin na Shugabannin Kasashe ne a shakara ta 2014 domin a lalubo hanyoyin bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.

Adesina ya kuma ce gabanin Buharin ya karbi kyautar, Shugaban zai halarci taron kasashen Afirka kan samar da zaman lafiya, inda zai ma gabatar da makala a wajen taron.

Kakakin ya kuma ce Buhari zai bar Najeriya ne ranar Litinin, sannan ana sa ran dawowarsa ranar Laraba.

Sanarwar ta kuma ce yayin ziyarar, Buhari zai sami rakiyar ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da na Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) da mai ba shi shawara an harkokin tsaro, Mohammed Babagana Mongunoda kuma Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriy, Ahmed Rufai Abubakar.