✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai raba wa manoma tallafin biliyan N600

Manoma miliyan 2.4 ne za su fara cin gajiyar tallafin na gwamnatin a rukunin farko

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, ta yanke shawarar bayar da Naira biliyan 600 a matsayin tallafin bunkasa harkokin noma.

Gwamnatin yayin raba tallafin kudin za ta maida hankali kan kananan manoma domin tabbatar da an samu wadatar abinci mai dorewa a fadin kasa.

Ministan Noma da Raya Karkara, Muhammad Sabo Nanono, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar gani da ido da ya kai katafaren kamfanin takin zamani na Dangote.

Ya ce domin tabbatar da amfani da kudaden yadda ya kamata, tallafin da za a bayar zai kasance ne na kayan noma ba tsabar kudi ba.

Ministan ya sake jaddada kudirin gwamnatin yayin wata ganawa ta musamman da ya yi da sauran kamfanonin takin zamani a birnin Iko, inda ya nemi su ba da hadin kai.

Nanono ya ce za a fifita kananan manona yayin rarraba tallafin inda a karon farko gwamnatin za ta fara da manoma miliyan 2.4.

Haka kuma Ministan ya misalta kamfanin Dangote a matsayin wani muhimmin ginshiki da zai tabbatar da cikar burin Gwamnatin Tarayya na kawo managarcin sauyi a fagen samun wadataccen abinci a kasar.

“Gwamnatin Tarayya tana so ta tabbatar dukkan ‘yan Najeriya sun samu wadataccen abincin da za su ci kuma ta hanya daya za mu iya cimma wannan manufa idan akwai wadataccen takin zamani.

“Ina matukar alfahari da Aliko Dangote dangane da ababe na ci gaba da yake yi wa kasar nan.

“Ina tunanin babu wani mutum da ya kwantanta irin hobbasan da yake yi wajen fannin zuba jari.

“Idan aka samu ko da wasu mutum biyu masu irin zuciyarsa, da kuwa an ga kyakkyawan sauyi a kasar nan”, inji Nanono.