✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai sake gina Kasuwar Sakkwato da ta yi gobara

Gwamna Tambuwal ya bukaci a tallafa wa ’yan kasuwar da suka yi asara

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin sake gina Babbar Kasuwar garin Sakkwato, mai shaguna 16,000 da gobara ta babbake a makon jiya.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya sanar da haka a ziyarar jajen da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya kai wa ’yan kasuwar da suka yi asara a gobarar.

Gambari ya yi bayanin ne bayan Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa ’yan kasuwar da ibtila’in ya shafi dukiyoyinsu.

Tambuwal ya shaida wa tawagar cewa gwamnatin Jihar ta gano musabbabin tashin gobarar wutar lantarki ne a taransfomar da ke cikin kasuwar da ake huldar kasuwanci da ita a duk Afirika.

Tambuwal ya ce “Kusan shago 16,000 ke a kasuwar, kashi 60% dinta ya kone a gobarar kuma wannan asarar babban abin damuwa ne ga mutanen jiha.

“Muna fatan samun tallafin Gwamnatin Tarayya musamman ga ’yan kasuwar da suka yi asara a cikin wannan yanayi na tsadar rayuwa,” a cewar Tambuwal.

Farfesa Gambari, ya ce sun kai ziyarar ce domin jajanta wa mutanen Sakkwato a madadin Shugaban Kasa, kuma su ga irin barnar da wutar ta yi.