✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai sake tafiya Landan ganin Likita

Wannan shi ne balaguro na biyu domin neman lafiya da shugaban zai yi a bana.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya sake tafiya birnin Landan domin ganin Likita.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mista Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis.

“Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan na Kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni domin a duba lafiyarsa.

“Ana sa ran zai dawo gida Najeriya a cikin mako na biyu na watan Yulin bana,” a cewar sanarwar.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne balaguro na biyu domin neman lafiya da shugaban zai yi a bana.

A ranar 30 ga watan Maris ne shugaban ya tafi birnin Landan, inda ya shafe makonni biyu kafin dawowarsa.

Babu shakka Buhari ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da har yanzu ba a bayyana abin da ke damunsa ba.

Buhari ya sake komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin likitansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.