✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai sayar da kamfanonin gwamnati 42

Kamfanoni da ma'aikatun da za a sayar sun hada da na ababen more rayuwa, noma, albarkatu, makamashi, da masana'antu

Gwamnatin Tarayya ta bayar da izimin sayar wa ’yan kasuwa wasu  ma’aikatu da kamfanoni  42 mallakin gwamnati.

Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE) ta ce tuni ta samu izinin sayar da ma’aikatun da kamfanonin daga Hukumar Cefanar da Kadarori ta Kasa (NCP), wadda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, yake jagoranta.

Kamfanonin da hukumomin gwamnati da za a sayar sun hada da: “11 a bangaren makamashi, 10 a bangaren masana’antu da ayyuka, takwas a bangaren noma da albarkatun kasa, sai 13 a bangaren abubuwan more rayuwa da hadakar gwamnati da ’yan kasuwa,” inji sanarwar BPE ta ranar Juma’a.

BPE ta sanar da haka ne bayan zaman da ta yi da Hukumar Cefanar da Kadarori Gwamnati a Fadar Shugaban Kasa, inda Hukumar ta amince da kundin tsare-tsaren BPE na aiwatar da aikin da na tara kudaden shiga da takaita tsautsayi a 2022.

Kundin dai ya kunshi bayanan yadda za a aiwatar da aikace-aikace da sauye-sauye da aka zayyana a ciki, kan ayyukan BPE na 2022.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kwamitin Asusun Gwamnati na Majalisar Dattawa, Sanata Mathew Urhoghide, ya karyata zargin da Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa ya yi wa BPE na almundahana.

Sanata Urhoghide ya sanar da hakan ne bayan Darakta-Janar na BPE, Alex A. Okoh, ya bayyana a gaban kwamitin, inda ya shaida mata cewa Ofishin bai tantance bayanan da ya samu ba kafin ya zargi hukumar da zarmiya.

Idan za a iya tunawa, ofishin ya zargi hukumar da kin sanya Dala miliyan 679.4 na kudaden shiga da ya tara daga tashoshin jiragen ruwa ba a cikin Asusun Gwamnatin Tarayya.