✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Ghana taron ECOWAS ranar Asabar

Buhari zai bar Abuja ranar Asabar domin halartar taron na ECOWAS karo na 59,

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Ghana ranar Asabar domin halartar taron Shugabannin Kasashe na Kungiyar Cinikkayyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) karo na 59.

Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce Shugaban zai bar Abuja ranar Asabar da nufin halartar taron na tsakiyar shekara, wanda takwarorinsa Shugabannin kasashen yankin za su halarta, in banda kasar Mali wacce aka dakatar a kwanakin baya.

Yayin taron dai, ana sa ran tsohon Shugaban Najeriya kuma Mai Shiga Tsakani na ECOWAS a kasar Mali zai gabatar da rahotonsa kan rikicin siyasar kasar.

Garba Shehu ya kuma ce taron zai karbi rahoto a kan sauye-sauyen da ake kokarin yi a yankin, yunkurin samar da takardun kudade na bai-daya da kuma kokarin da suke yi na mayar da tsarin takarar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka ta AU tsakanin mambobin ECOWAS karba-karba.

Yayin ziyarar dai, Shugaba Buhari zai sami rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Zubairu Dada, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire da kuma Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed.

Sauran masu rufa wa Shugaban baya yayin taron sun hada da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da kuma Babban Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Sanarwar ta ce ana sa ran Shugaban da ’yan tawagarsa za su dawo Abuja bayan kammala taron.