✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Guinea Bissau ranar Alhamis

A gobe Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga birnin Abuja zuwa Bissau domin halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yanci ta Jamhuriyyar Guinea Bissau a…

A gobe Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga birnin Abuja zuwa Bissau domin halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yanci ta Jamhuriyyar Guinea Bissau a ranar 24 ga watan Satumba.

Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaban Kasar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba.

Tawagar Shugaba Buhari ta kunshi manyan jami’an Gwamnati da suka hadar da Ministan Harkokin Wajen, Geoffery Onyeama; Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya); Babban Ma ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa, Manjo Janar Babagana Monguno da kuma Darekta Janar na Hukumar Leken Asiri, Ahmed Rufai Abubakar.

Shugaban Kasar tare da Shugabannin Kasashen Cote d’ Ivoire, Rwanda, Mauritania, Togo da Liberia za su halarcin bikin yayin da makociyar kasar ta cika shekaru 47 da samun ‘yanci.

Yayin da Shugaba Buhari zai kasance a birnin Bissau, zai kuma kaddamar da wani sabon titi da Gwamnatin Kasar ta yi masa karamcin rada wa titin sunansa.

Zai kuma halarci wat liyafa tare da sauran Shugabannin Kasashen wadda Shugaba Umara Sissoco Embalo na Guinea Bissau  zai dauki nauyi.

Kyakkyawar dangartakar da ke tsakanin Najeriya da Guinea Bisauu ta samo asali ne tun a shekarar 1974.