✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Paris halartar taron kasashen Afrika

Za su tattauna kan tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi da kuma tattalin arziki.

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Paris, babban birnin Faransa ranar Lahadi, don halartar Taron Kasashen Afirka na kwana hudu.

Taron zai mayar da hankali kan tattalin arzikin Afirka, saboda nakasun da cutar coronavirus ta kawo ga nahiyar, tare da nemo mafita ga bashin da ake bin kasashen.

Taron, wanda Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai dauki nauyin gudanarwa, zai tattaro manyan masu ruwa da tsaki a cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da wasu shugabannin gwamnati na duniya.

Abin da taron zai mayar da hankali a kai

Taron na da nufin nemo hanyar hada kai, samar da kudade daga waje da bashi ga Afirka, da kuma sake fasalin kamfanoni masu zaman kansu.

A yayin ziyarar, Shugaba Buhari, zai gana da Shugaba Macron kan matsalar tsaro da ta addabi yankin Sahel da yankin Tafkin Chadi.

Za kuma su tattauna batun siyasa, kiwon lafiya, da kuma yadda COVID-19 ta kawo tsaiko ga kasashen Afrika.

Buhari zai gana da wakilan Majalisar Tarayyar Turai

Buhari zai kuma gana da manyan wakilan Majalisar Tarayyar Turai, game da harkar iskar gas da kuma tsaro a tsakanin kasashen majalisar.

Jami’an gwamnati da za su yi masa rakiya su ne Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama; Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed; Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Adebayo; da Ministan Lafiya, Osagie Ehanire.

Akwai kuma Mashawarci Kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno; da kuma Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa,  Ahmed Rufa’i Abubakar.