✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ranar Alhamis

A gobe Alhamis 1 ga watan Oktoba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ta gidan talibijin na kasa (NTA) a maimakon…

A gobe Alhamis 1 ga watan Oktoba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ta gidan talibijin na kasa (NTA) a maimakon Dandalin Eagle wanda a baya aka sa ran a nan zai yi.

Mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina ya fitar da hakan cikin wata sanarwa yana mai cewa Shugaban Kasar zai yi jawabin ne da misalin karfe 7.00 na safe wanda hakan na daya daga cikin sha’anin da za a yi na munar cikar kasar shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Adesina ya ce daga na shugaban zai garzaya Dandalin Eagle wurin taron murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan inda zai kalli faretin jami’an tsaro da sauran shagulgula da za a fara da misalin karfe 10.00 na safe.

A cikin sabuwar sanarwar, Adesina ya ce ‘yan Najeriya su yi watsi da sanarwar baya wadda ta nuna cewa shugaban zai yi jawabin ne a gaban jama’a a Dandalin Eagle.