✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhun albasa ya kai N22,000 a Kwara

“Albasar N100 yanzu bata isa ta yin girki. Wacce na siya ta N500 yanzu a da ita nake saye N100.”

Matakin da manoman albasa a Arewacin Najeriya suka dauka na rage yawan albasar da suke kaiwa zuwa Kudancin Najeriya ya sa farashinta ya yi tashin gwauron zabi a Jihar Kwara.

Hakan dai ya sa mazauna Jihar da dama dole suka kara yawan kudaden da suke kashewa wajen sayen albasar, wacce daya ce daga cikin kayan lambun da aka fi amfani da su a girke-girke.

Kungiyar Monoma da Dillalan Albasa ta Najeriya (OPMAN) dai ta sanar da daukar matakin a kwanakin baya saboda karuwar matsalar tsaro da kuma barazanar da ake yi wa mambobinta a yankin.

Farashin albasa dai a Jihar ya yi tashin gwauron zabi da kusan kaso 200 cikin 100, kamar yadda bincike Aminiya ya gano a kasuwannin Ilorin, babban birnin Jihar.

A kasuwar Yoruba Road misali, masu saye da masu sayar da albasar sun koka kan karancinta ke ci gaba da ta’azzara a Jihar.

Wani dilan albasar a kasuwar, Malam Garba Dogo ya ce, “Yawanci farashin albasa kan tashi a irin wannan lokacin saboda shine lokacin da manoma a Arewa suke girbinta, amma a wannan karon dakatar da safarar ta ne ya dada ta’azzara lamarin.

“Buhun da a baya ake sayarwa N14,000 yanzu ya koma N22,000,” inji shi.

Ita ma wata ma’aikaciyar gwamnati da ta je kasuwar domin sayen albasar, Grace Agboluaje, ta koka kan cewa yanzu ta N100 bata isarta yin girki.

“Albasar N100 yanzu bata isa ta yin girki. Wacce na siya ta N500 yanzu a da ita nake saye N100,” inji ta.

Ita ma wata mai sayen albasar, Idowu Salako ta ce, “Ya kamata gwamnati ta shiga tsakani ko ma samu farashinta ya sauko.

“Yadda abubuwa suka koma yanzu, albasar ta yi karanci, wacce ake samu kuma ta yi tsada, gwamnati kuma ta ki yin wani katabus wajen lalubo bakin zaren, musamman wajen magance hare-haren da dillalanta suka yi ikirarin ana kai musu,” inji Salako.

A kasuwar Ipata ma, Malama Rafatu Mohammed ta ce abin takaici ne yadda aka dakatar da kai albasar wasu sassa na Najeriya.

“Kusan kwana takwas kenan ba a kawo ta Jihar Kwara ba. Abubuwa sun yi tsada a nan. Kwandon N800 a baya yanzu ya koma N1,300.”

Kazalika, a kasuwar Mandate ma labarin haka yake, domin buhun N9,000 yanzu ya koma tsakanin N20,000 zuwa N22,000, kamar yadda Amina Ibrahim, wata dilar albasar ta shaida.