✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bukukuwa: An haramta tayar da abubuwa masu kara a Nasarawa

Kwamishinan 'yan sandan ya yi gargadi ga iyayen yara cewar, za a hukunta duk wanda ya karya dokar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa Bola Longe, ya hana tayar da abubuwa masu kara yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a Jihar.

Ya ba wa jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro na jihar umarni da su sanya ido da kuma hana amfani da knockout.

Ya kirayi iyaye da su ja wa ’ya’yansu kunne, da su guji wa amfani da abubuwan fashewa yayin bukukuwan domin duk wanda aka kama ya karya dokar zai fuskanci hukuncin hukuma.

Bola Longe, ya kara da cewa an ba ofisoshin rundunar a dukkanin yankunan jihar umarnin tabbatar da tsaro a lokutan bukukuwan.

Ya kara da bayar da lambobin tuntubar rundunar domin agajin gaggawa: 08112692680, 08108795930, 08037461715.