✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bulama Bukarti ya zama kwararren lauya a Birtaniya

Bulama Bukarti zai iya aiki a matsayin kwararren lauya a yankunan Wales da New England

Barista Audu Bulama Bukarti, shahararren lauya nan mai fafutikar kare hakkin dan Adam da marasa galihu, ya tsallake matakin samun lasisin aiki a matsayin kwararren lauya a kasar Birtaniya.

Barista Bulama Bukarti ya tsallake mataki na biyu wanda kuma shi ne na karshe na samun izinin fara aiki a matsayin kwararren lauya a yankunan Wales da New England na Birtaniya.

Da yake taya Bukarti murna, shahararren dan jarida kuma Editan kafar yada labarai ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya ce, “Farin cikina ba zai misaltu ba da na samu labari cewa abokin aikinmu kuma dan uwa Audu Bulama Bukarti ya tsallake matakin karshe a Shirin Musayar Kwararrun Lauyoyi;

“Yanzu zai iya neman lasisin aiki a matsayin kwararren lauya a yankin Ingila da kuma Wales. A takaice, zai iya aiki a matsayin lauya a wadannan yankuna.”

Kwarewar Bulama Bukarti

Barista Bulama Bukarti, ya yi fice wajen bincike da fashin baki a kan ayyukan ta’addancin Boko Haram, kungiyar da ta addabi yankin da ya fito, wato Arewa maso Gabashin Najeriya.

A watan Satumban shekarar 2020 ne dai Cibiyar Tsara Dabaru, Nazari da Bincike kan Harkokin Tsaro na Kasa da Kasa (CSIS) ta nada Audu Bulama Bukarti a matsayin babban lauyanta.

Bukarti gogaggen lauya ne dan asalin Gasua a Jihar Yobe, amma ya yi karatu kuma yake zaune a Jihar Kano, kafin tafiyarsa CSIS.

An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1984, kuma ya fara aikin koyarwa a Jihar Yobe bayan kammala Karatun Kwarewa a Fannin Malanta (NCE).

Daga bisani ya koma Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ya yi karatu a Tsangayar Koyan Aikin Lauya, wanda ya kammala a 2011.

Daga nan ya shiga aikin lauya gadan-gadan, inda ya rika tsayawa domin kare marasa galihu kyauta.

Barista Audu Bulama Bukarti ya yi fice a lokacin zanga-zangar yaki da karin farashin man fetur da aka yi a shekarar 2011 a Najeriya, inda ya tsaya wa wasu matasa da aka kama.

Ya ci gaba da aikin lauya, tare da fafutukar kare hakkin jama’a, har zuwa 2014 lokacin da ya sami aikin koyarwa a Tsangayar Koyar da Aikin Lauya ta Jamiar Bayero.

A halin yanzu dai Babban Lauya ne a cibiyar CSIS.