✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bunkasa noman rani zai kawar da fargabar yunwa a Najeriya a 2023 – Masani

Ya ce yin hakan zai rage barazanar yunwa a 2023

Wani babban manomi a Zariya, Malam Ahmed Abubakar, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta samar da tallafin aikin norman rani ga manoma don rage radadin ambaliyan ruwa da kuma kauce wa fargabar yunwan da ake hasashe a shekarar 2023.

Ya yi wannan kira ne a zantawarsa da Aminiya a Zariya, inda ya ce ambaliyar ruwa ta share amfanin gona mai yawan gaske a Najeriya, a shekarar da ta gabata.

Ya yi nuni da cewa ambaliyar ta yi kama da wadda aka samu a shekarar 2012, amma tallafin kayan noman rani da aka samu daga gwamnatin wancan lokacin ya rage radadinta tare da taimakawa wajen daidaituwar farashin abinci, duk da lalata amfanin gona mai yawa da ambaliyar ta yi.

“A matsayinmu na manoma muna kira ga Gwamnati da ta maimaita irin tsarin da ta yi a shekarar 2012 nasSamar da kayan aikin noman rani da wurwuri dan rage radadin ambaliyar bara wadda ke barazanar kawo yunwa domin damar da isasshen abinci a shekarar2023,” manomin.

Malam Ahmed ya kuma ce rashin samun ruwa sama da wuri, da kuma daukewar ruwan da wuri shi ne ya kawo shinkafar ba ta samuwa kamar yadda ya kamata, ga kuma tsutsotsin da a baran ya ce da suka lalata shinkafar noman daminar.

Ya ce ya ga manoman da suka shuka irin har buhu hudu zuwa biyar, amma ba su sami ko da abin da suka shuka ba.

Sai dai ya ce, “Ana sa ran masara zata yi kyau kwarai duk da tsadar takin zamani da monoma suka fuskanta a shekarar damunar da ta gabata, kuma wannan nasarar ta samu ne saboda da manoma sun yi shuka da wuri kafin kasar ta yi sanyi.

“Don haka manoma sun samu amfanin gona mai inganci a bara, don haka babu batun yunwa kamar yadda ake fargaba a shekar 2023.”

Manomin ya kuma ce duk da cewa manoman sukan shuka wake a duk inda suka shuka masara saboda da su inganta aikin noman nasu, shi ma waken ya fuskanci kalubalen daukewar ruwan sama da wuri wadda ya zo da alamun hunturu a wannan shekarar.

‘Duk da haka bai kamata a bude iyakokin Najeriya ba’

Ya kuma ce duk da cewar ambaliyan ta fi shafar gonakin shinkafa ne, amma bai goyi bayan bude kan iyaka dan shigowa da abinci ba.

Malam Ahmed ya kuma ce kididdiga ta nuna cewa Najeriya tana bukatar tan miliyan bakwai na shinkafa a kowace shekara, amma kafin ambaliyar bara, Najeriya tana samar da sama da tan miliyan biyar na shinkafa.

A cewar Ahmed Abubakar, idan aka samar da kayan aikin noman rani a JIhohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Nasarawa da kuma Jigawa, Najeriya za ta samar da shinkafar da take bukata a sabuwar shekarar 2023.