✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buratai na ganawar sirri da kwamandojin soji

Kwamandojin sojin Najeriya na ganawar sirri kan yanayin tsaron da kasar ke ciki

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai na ganawar sirri da manyan kwamandojin rundunar kan halin tsaro da kasar ke ciki.

Taron sirrin da ke gudana ne a Hedikwatan Tsaron Najeriya da ke Abuja zai tattauna ne kan zanga-zangar #EndSARS, harbin da ake zargin sojoji da yi a taron masu zangar-zangar a Lekki da sauran batutuwa.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeiya, Kanar Sagir Musa ce taron zai mayar da hankali ne kan “yanayin da tsaron kasa ke ciki da sauran batutuwa masu alaka da shi”.

Shugabannin manya da Rundunonin Soji da kwamandojin rundunar ne ke halartar taron a daidai lokacin zanga-zangar ta #EndSARS ta rikide zuwa tashin hankali da farfasa ma’adanar kayan abinci ana sacewa.