Daily Trust Aminiya - Burina in inganta rayuwar marayu da marasa galihu – Hajiya A
Subscribe

Hajiya Adama tare da ’yarta da waxansu marayun da take kula da su

Burina in inganta rayuwar marayu da marasa galihu – Hajiya Adama Muhammad

Hajiya Adama Muhammada wadda aka fi sani da (MD Lawan) ita ce tsohuwar shugabar Kungiyar Mata Musulmi (FOMWAN) ta Jihar Borno. Mace ce mai goya marayu, wacce ta rike tare da ilimantar da marayu fiye da 50 har zuwa matakin jami’akuma ta aurar da su. A tattaunawarta da Aminiya ta fadi yadda ta samu kanta cikin wannan aiki na jinkai.

Tarihin rayuwata?

Sunana Adama Muhammad, mahaifina shi ne MD Lawan kamar yadda ake kiransa kuma yana nan a raye, mahaifiyata kuma sunanta Zainab ta rasu kamar shekara 27 da suka shige.

An haife ni a garin Biu  a 1964 na fara karatu a makarantar firamare  ta Gamboru, bayan an yi wa mahaifina canjin wurin aiki zuwa nan Maiduguri, daga nan na  shiga Kwalejin ’Yan mata (GGC) ta Maiduguri, inda na kammala a 1983. Daga nan na je Jami’ar Maiduguri na yi Diploma kan Nazarin Addinin Musulunci na gama  a 1985, sai na yi aure. Bayan shekara daya na sake komawa jami’ar na yi digiri a fannin Nazarin Addinin Musulinci, na yi hidimar kasa (NYSC) a nan Maiduguri, ina kammalawa na samu aiki da Kwalejin Ilimi ta Sa Kashim Ibrahim a 1991. Bayan na fara aiki sai na sake komawa na yi digiri na 2 a 1995 kuma har yanzu ina aiki a wurin.

Yadda na shiga harkar taimaka wa addini

Alhahamdulillah da farko dai zan gode wa mahaifana musamman mahaifiyata kan yadda tun ina karama suka cusa min son addini da taimakon al’umma a zuciyata. Tun muna firamare malamanmu suke yi mana gargadi a kan kada mu yi wasa da karatu, to tun daga wancan lokaci na maida himma wajen karatu da kaunar addini domin mukan je wuraren tarurruka na addini irin su Mauludi muna yin karatun Alkurani da wake-wake. Na fara shiga cikin harkokin addini tunda daga makarantar sakandare, a Kungiyar Dalibai Musulmi (MSSN). Na kasance mamba a kungiyar aka hada ni da wata ’yar uwa a Musulunci wacce take gaba da ni ta rika nuna min yadda al’amura suke  a kan harkar addini na samu karuwa sosai. Har ta kai akan shirya mana taro a dakin taro na makaranta a kowacce ranar Asabar ana yi mana nasiha da karance- karance da kuma gabatar da kasidu akan rayuwar shugabannin addini, wadda manyan malaman da ake gayyata suke gabatarwa irin su Sheikh Muhammad Abba Aji da Sheikh Sa’adu Ngamdu da Shiekh Usman Bida da Sheikh Ibrahim Sale da  sauran manyan malamai. Daga irin nasihohin da malaman ke yi mana sai na kara sha’awar son hidima ga addini da kuma taimakon marayu da marasa galihu. Al’amarin MSSN ya yi babban tasiri a rayuwa ta wajen ba da gudunmawa ga ci gaban addinin Musulunci. Ba zan taba mantawa ba ina aji uku 3 aka zabe ni in je gasar kacici kacici a Gidan Talabijin na Kasa (NTA) na  Maiduguri, kuma na samu nasara na zo ta daya har aka ba ni kyautar fanka. Na halarci tarurruka da dama tun ina makarantar sakandare a Kungiyar MSSN zuwa jihohi irin su Bauchi.

Har ta kai na zama Shugabar Kungiyar MSSN a makarantarmu, haka zalika da na shiga jami’a na ci gaba da wannan gwagwarmaya na fadakar da ’yan uwa mata a kan kada su jefa kansu cikin halaye marasa kyau don suna jami’a, kullum aikin ke nan, idan ba na wurin daukar karatu to muna masallaci. Gaskiya babu abin da mutum zai ce sai godiya ga Ubangiji bisa wannan baiwa da Ya yi min.

Sakacin matasa wajen kula da addini

Wannan zan dora wa iyaye da malamai laifi, domin hakki ne a ba da kula a kan tarbiyyar yara, musamman a halin da muke ciki a yanzu. Domin akwai aya da Allah Yake cewa bai hallicci aljani da mutum ba sai dai don su bauta masa, saboda haka kamata ya yi iyaye da sauran al’umma su rika kula da duk irin halin da suka ga ’ya’yansu a ciki, kuma su rika binciken duk wani motsi da suke yi. A gaskiya yadda a yanzu matasanmu suke ciki abin takaici ne, wajibi ne su tsaya su kusantu ga dabi’u na addini da kuma taimaka wa al’umma. Don haka ne ni a kullum nakan tuna da ayar da Allah Yake cewa kowace rai za ta dandani mutuwa, saboda haka sai mutum ya tashi tsaye domin neman lahirarsa. Ko a nan duniya kana son gida mai kyau da abin hawa mai kyau, to don me  ba za ka tashi ka yi kokari ba wajen neman lahirarka? Don haka shawarata ga matasa ita ce su tashi tsaye don taimakon kansu ta hanyar da ta dace, kuma su guji fadawa cikin munanan dabi’u da suka saba wa koyarwar addini. Kuma duk abin da za ka yi ka yi shi don Allah, ka kuma duba wane abin amfani ka yi domin ci gaban al’ummarka shi kuma wannan abu ka yi ba wai don mutane ba, a’a ka yi don Allah ka tabbatar ka bar wani abu da jama’a za su amfana da shi.

Hajiya Adama Muhammad
Hajiya Adama Muhammad

Yadda na fara tallafa wa marasa karfi

Gaskiya tun ina karama nake son tallafa wa marasa karfi a tsakanin al’umma, hakan ya sa na tashi da wannan buri a rayuwata, kuma alhamdullahi, domin duk da cewar na yi aure, amma Allah cikin ikonSa bai ba ni haihuwa ba, sai bayan shekara 20, Allah Ya ba ni ’ya mace kuma ita ke nan nake da ita, a yanzu haka. Amma da yake na kudiri aniyar tallafa wa al’umma, na kasance  tunda na fara aiki ba zan iya tuna yaushe na taba saya wa kaina abin da ya kai na Naira dubu biyar daga albashina ba, sai dai bukatun al’umma. Amma Allah cikin ikonSa sai in samu abin da ya fi albashin nawa, don wannan fada ce ta Ubangiji duk wanda ya bayar Allah zai ninka masa, don haka duk wanda ya ke tallafa wa al’umma, insha Allahu sai ya ga fiye da abin da ya yi mutukar don Allah yake yi da kuma ikhilasi.

Na dauki nauyin yara marayu da marasa karfi kusan 50 wadanda na rike su, kuma na sa su a makaranta har matakin jami’a, kana na aurar da matan, wadansu mazan kuma sun zama mutanen kansu suna aiki. Kuma yanzu haka a gidan nan akwai wadansu marayu fiye da 10 ina tare da su. Duk wannan ina yi ne domin Allah, kuma har yau ban fasa ba. Kamar yadda na fada tun a can baya Allah Ya arzurta ni da miji mai son taimakon al’umma wanda shi ma yana daga cikin wadanda suka taimaka, haka muka rika

yi, da shi tsawon lokaci, har Allah ya karbi ransa, (Allah Ya jikansa da rahama). Haka zalika shi kansa mijina da nake tare da shi a yanzu shi ma hakan yake wajen kokarin tallafa wa marayu da masu karamin karfi. To ka ga ba ni da abin da zan ce, kuma ba wai na fadi haka ba ne don riya, sai dai don jama’a su yi koyi da hakan ko su aikata abin da ya fi haka.

A Kungiyar FOMWAN

A fannin Kungiyar FOMWAN mun ba da tallafin karatu ga mutum fiye da 1,000 marasa karfi da marayu, har yanzu abin da na fi sha’awa shi ne in ga na sa wani ya yi dariya na faranta wa wani rai. A ce ya ji dadi ta dalilina, kuma a kullum ina rokon Allah in mutu a kan wannan hali  na son taimakon al’umma.

Shawara ga masu karfi kan daukar nauyin marayu

Ganin yanzu ga marayu sun yi yawa dalilin yakin Boko Haram da ya yi sanadiyar rashin iyayensu, wannan lamari abin da mutum zai zauna ne ya yi kuka. Irin halin da za ka ga yara kanana suna ta gararamba a kan tituna alhali ya kamata a ce suna makaranta ne amma hakan ya gagara, ga shi muna da masu halin da za su iya daukar nauyin yara da dama. Shawarata ga al’umma ita ce mu rika taimakon jama’a da nuna musu kauna da jin tausayin na kasa da mu. Yanzu misali sai ka ga mutum yana hawa mota ta miliyoyin Naira,  amma ga makwabtansa da ’ya’ya marayu  wadanda suke bukatar taimakonsa, amma bai yi ba. Ya kamata ya yi tunani, ya dauki nauyin wadansu da rabin kudin wannan mota, Ina ganin samar da ilimi ga  yara shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, don haka jama’a idan mun samar wa yara ilmi to hakika za mu samu kyakkyawan ci gaban da kowace al’umma take bukata, Misali irin halin da muka tsinci kanmu a ciki a nan Maiduguri abu ne da yake bukatar kowa ya ba da gudunmawarsa, domin yin hakan zai bamu damar sauke nauyin da Allah Ya dora mana,

More Stories