✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burkina Faso ta amince da mulkin soji na shekara uku

Shugaban dakarun sojin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka kulla da masu ruwa da tsakin kasar.

Sojin da ke jagoranci a kasar Burkina Faso sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mulkin shekaru uku gabanin damka ragamar mulki ga fararen hula wata guda bayan juyin mulkin kasar da ya hambarar da shugaba Roch Marc Christian Kabore.

Bayan doguwar tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki na Burkina Faso ciki har da kungiyoyin fararen hula da bangarorin tsaron kasar, da aka fara a ranar Litinin zuwa Talata ne aka tabbatar da matsayar ga manema labarai.

Jagoran mulkin sojin na Burkina Faso Laftanal-Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar mulkin wadda ta sahale masa jagoranci har nan da watanni 36 kafin Babban Zaben kasar.

Matakin na zuwa ne bayan taron majalisar tsaron kasar ya saba da kudirin farko na mulkin watanni 30 da sojojin suka gabatar kafin mayar da kasar turbar dimokuradiyya.

Taron ya kuma kunshi jam’iyyun siyasa da kungiyoyin matasa da na mata, sannan wakilcin daukacin mutanen da hare-haren ta’addancin ya raba da matsugunansu a sassan kasar tun daga 2015 zuwa yanzu.