✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CAN ta dakatar da shugabanta kan taya Pantami murnar zama farfesa

Rabaran Sunday Congo ya sauka daga mukaminsa bisa umarnin uwar kungiyar.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta dakatar da shugabanta na riko a Jihar Gombe, Rabaran Sunday Congo, kan aike wa Ministan Sadarwa, Isa Ibrahim Pantami, sakon taya murna kan matsayin Farfesa da ya samu.

Tuni Rabaran Sunday Congo ya sauka daga mukaminsa bayan samun umarnin  daga uwar kungiyar, wadda ta ce ta dakatar da shi ne saboda ba da izinin Shugaban Kwamitin Zartarwarta ya aike da sakon ba.

A takardarsa ta sauka daga mukaminsa, Rabaran Congo ya ce, “Na samu wasikar uwar kungiyar CAN reshen Arewa maso Gabas cewa an dakatar da ni daga aiki saboda na taya Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, murna, wanda kuma na yi ne da kyakkyawar manufa.”

A wasikar da ya aike wa Pantami ranar 6 ga Satumba, 2021, Rabaran Congo,  ya bayyana ministan — wanda dan asalin Jihar Gombe ne — da cewa muna “alfahari” da Pantami a matsayin “danmu”.

  1. – Laifin taya murna

Amma a ranar 15 ga Satumba, 2021, Babban Sakataren CAN na Kasa, Barista Joseph Daramola, ya fitar da sanarwa cewa shugaban rikon kungiyar na Jihar Gombe, bai nemi izinin uwar kungiyar ba kafin ya tura sakon taya murnar.

Takardar dakatarwar ta ce, “Muna sanar da kai cewa sakon taya murna da ka aike wa Ministan Sadarwa, Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami, ta haifar da damuwa a tsakanin mambobin kungiyar CAN.

“Gaban kanka da ka yi ba tare da nema ko samun izini ba, tsokana ce da yunkurin yin zagon kasa ga Kwamitin Zartarwar kungiyar CAN.

“Abin da ka yi ba da yawunmu ba ne, ta kowace fuska, ana kuma umartar ka da ka sauka daga mukaminka a Kwamitin Zartarwar CAN a Jihar Gombe nan take, ka mika duk kayan kungiyar da ke hannunka ga mai bi maka a matsayi.

“Ana shawarartar ka da cewa nan gaba ka tuntuba ka nemi izini, idan uwar kungiya ta ba ka sai ka yi, domin mu rika magana da murya daya.”

  1. – Takaddamar ba wa Pantami Farfesa

Jami’ar Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya da ke Owerri a Jihar Imo (FUTO), ce ta ba wa Pantami matsayin Farfesa a fannin ilimin Tsaron Intanet.

Wasu malaman jami’a dai sun kalubalanci hakan, da cewa ministan bai cancanta ba tunda bai taba koyarwa a jami’ar ba, kuma matsayin farfesa ana bayar da shi ne kawai bisa la’akari da yawan bincike rubuce-rubuce da aikace-aikace da kuma koyarwa a aji da wanda aka ba wa ya yi.

  1. – Babu batun addini

A shekarar 20219 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Pantami a matsayin ministan da ke wakiltar Jihar Gombe.

Da yake bayani game da dakatawar, Daramola ya ce CAN ta sha taya Musulmi murna a daidaikunsu ko a kungiyance.

A cewarsa, dakatarwar ba ta da wata alaka da addini face yunkurin kungiyar na tabbatar da da’a da kiyaye ka’ida a cikin kungiyar.

Ana ganin CAN na taka-tsantsan ne saboda wasu rahotanni da a baya suka nuna damuwa game da matsayinsa a kan kungiyar Taliban.

Masu wadannan bayanan a wancan locaki sun yi ta neman ya sauka daga mukaminsa, saboda a cewarsu, wasu karatuttuka da ya yi kimanin shekara 20 da suka gabata, sun nuna yana goyon bayan ayyukan Taliban.

Sai dai ministan ya fito ya nemi afuwa game da hakan, inda ya ce rashin fahimta da gogowar rayuwa  ce ta sa shi yin hakan a baya.

Ya kuma yi burus da masun neman ganin sai ya sauka daga mukamin nasa.