✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canada na hana daliban Najeriya biza

Ofishin Jakadanncin Najeriya  a kasar Canada ya yi korafin cewa kasar na hana dalibai da sauran ‘yan Najeriya bizar shiga kasar ba bisa adalci ba.…

Ofishin Jakadanncin Najeriya  a kasar Canada ya yi korafin cewa kasar na hana dalibai da sauran ‘yan Najeriya bizar shiga kasar ba bisa adalci ba.

A jawabin Jakadan Najeriya a Canada, Ambasada Adeyinka Asekun ga taron da ofishin ya shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ‘yanci, ya ce kasashen biyu na kokarin magance matsalar da kuma neman ganin ana mutunta ‘yan Najeriya a kasar.

“Abu mafi muhimmanci shi ne ana fatar yarjejeniyar za ta magance matsalar yadda ake hana ‘yan Najeirya da dama biza alhali sun cancanci a ba su”, inji shi.

Jakadan ya ce ‘yan Najeriya da dama na sha’awar zuwa Canada domin neman ilimi amma ana hana su izinin shiga kasar ba bisa adalci ba.

Canada na daga cikin kasashen da daliban Najeriya masu hali ke son zuwa domin halartar manyan makarantu, saboda yadda yawan yajin aiki ke kawo tsaiko ga karatu a manyan makarantun Najeriya.

Ambasada Asekun ya ce matsalar za ta zama tarihi da zarar sabuwar yarjejeniyar ta fara aiki tsakanin kasashen da suka dade suna amfanar juna tun 1960.

Ya yaba da gudunmuwar Canada ga Najeriya musamman na kafa dakin gwajin cututtuka masu yaduwa a Legas a 2014, lokacin da aka samu bullar cutar Ebola. Dakin gwajin ya taimaka gwargwajo wajen yaki da cutar COVID-19.