✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi: Buhari ya talauta mu baki daya —Kwankwaso

Ya ce baki dayan ’yan takara sun talauce saboda sauyin kudin da Buhari ya yi

Dan takarar ahugaban kasa a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce sake fasalin Naira da Gwamnatin Buhari ta yi ya talauta dukkan ’yan takarar da ake da su.

Kwankwaso ya ce a halin da ake ciki, matsayinsu daya da takwarorinsa, wanda hakan zai ba shi damar lashe zabe cikin sauki.

“Mun ji mutane na yi mini ba’ar cewa Rabiu Kwankwaso ba shi da kudi (na yin kamfe), sai ga shi yau Shugaban Kasa ya talauta baki daya ’yan takara.

“Don haka, baki dayanmu matalauta ne, mun zama daya,” in ji shi.

Dan takarar ya bayyana haka ne ta cikin wani shiri da Tashar Rediyo ta Dandal Kura da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ta yi da shi a ranar Laraba.

Ya ce kafin wannan lokaci mutane na yi masa ba’ar ba shi da kudin da zai yi takarar shugabancin kasa.

Ya ce matakin canjin kudi da Gwamnatin Tarayya ta dauka ya  talauta kowa, ciki har da abokan hamayyarsa.

Game da yiwuwar ya lashe zabe, Kwankwaso ya ce gani ya kori ji a lokacin da ya yi Gwamnan Kano na wa’adi biyu da kuma minista da sanata.

A can baya, an ambato Kwankwaso na cewa game da sake fasalin Naira, “Abin da na sani matakin ba mai kyau ba ne ga kasa.

“’Yan Najeriya sun cancanci rayuwa cikin aminci da kauna daga shugabanninsu.

“Amma jefa ’yan kasa cikin matsi, na yi amannar hatta su kansu shugabanni ba zai yi musu kyau ba balle kuma talakawa.”