✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin Kudi: Buhari ya yi mana maganin gwamnonin APC —Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki gwamanonin APC da ke sukar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan dokar sauyin takardun…

Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki gwamanonin APC da ke sukar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan dokar sauyin takardun kudi.

Kwankwaso ya ce maganganun da gwamnonin ke yi a baya-bayan nan kan dokar sun ba shi mamaki kwarai, musamman yadda suke cin mutuncin shugaban kasar.

“Kawai sai muka ji sun buge da zagin jagorori, abin daure kai ma shi ne har da shugaban kasa, abin da ban taba kawowa za su iya aikatawa ba.

“Na yi mamakin kalaman da ke fita daga bakinsu, har na fara tunanin me ke damunsu haka? Watakila akwai kamshin gaskiya a batun da EFCC cewa suna jiye da biliyoyin kudi a gidajensu.

“Yanzu wannan dokar ta sanya duka wani kudin sata ya zamo mara amfani, watakila abin da ya bata musu rai ke nan, don haka muna farin ciki da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi a wannan karon.

“Da haka nake bai wa sauran hukumomi shawara da su sanya ido kan wadannan mutanen, kuma ina so in tabbatar muku da cewa jam’iyyarmu za ta taimaka wa Gwamnatin Tarayya ranar zabe.

“Ku gaya wa duk ’yan NNPP su shiga EFCC, su shiga wurin da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suke (ranar zabe), duk inda suka ga ana kokarin sayen kuri’u, su hana,” in ji Kwankwaso.