✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Canjin Kudi: Jami’iyyu 13 za su kaurace wa zaben 2023

13 daga cikin jam'iyyun siyasa 18 da ake da su a Najeriya sun yi barazanar kaurace wa babban zaben 2023 da ke tafe saboda canjin…

13 daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ake da su a Najeriya sun yi barazanar kaurace wa babban zaben 2023 da ke tafe saboda canjin kudin da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Jami’iyyun sun ce ba za su shiga zaben ba, muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) bai kara wa’adin amfani da tsoffin takardun kudi ba.

Sai dai shugabannin jami’iyyan sun yaba wa Shugaba Buhari kan sauya fasalin takardun kudaden, amma suka bukaci a kara wa’adin da aka kayyade na amfani da tsoffin.

Sun kuma soki, gwamnonin jami’iyyar APC mai mulki uku da suka maka shugaban kasa a kotu domin neman kara wa’adin karbar tsoffin kudin.

Gwamnonin su ne Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna daYahaya Bello na Kogi da kuma Muhammada Bello Matawalle na Zamfara)

CBN dai ya sanya 10 ga watan Fabrairun da muke ciki a matsayin wa’adin amfani da tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200.

Tuni kuma ya umarci bankuna da su fara bayar da sabbin kudaden a bisa kanta.