✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi: Kayan Abinci Da Dabbobi Sun Fadi Warwas A Yobe

Kayan masarufi da dabbobi sun fadi da fiye da rabi a kasuwannin jihar

Hada-hadar kasuwanci na tafiyar hawainiya a kasuwannin Jihar Yobe sakamakon canza fasalin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

Aminiya ta gano a yanzu haka, kayan masarufi da dabbobi sun fadi da fiye da rabi a kasuwannin jihar.

Alal misali, farashin babban mudun gero ya fadi warwas a warwas a kasuwar garin Dawasa da ke Karamar Hukumar Nangere, inda ranar Alhamis farashin babban buhu ya fadi zuwa Naira dubu takwas sabanin dubu 19 da ake sayarwa a watan jiya.

Haka nan farashin babban mudun wake bai wuce Naira 500 ba. Yanzu buhu ya koma N16,000 zuwa N17,000 maimakon Naira dubu 35 zuwa 37,000 da ake sayar da shi a watan jiya.

Dabbobi sun yi arha

A bangaren dabbobi kuwa wani mazaunin garin na Dawasa, Malam Babayo Dawasa ya bayyana wa Aminiya cewa ragon da a watan jiya aka saye shi a kan Naira dubu 30 a yanzu bai wuce Naira dubu 15 ba.

Haka nan akuyar da a mako biyu da suka wuce aka saye ta a kan Naira dubu 35 a yanzu farashin ta ba zai wuce Naira dubu 17 ba ba koma kasa da haka.

Kaya sun karye a kasuwar Geidam

A ranar Laraba a babbar kasuwar Geidam da ke kan iyaka da Jumhuriyar Nijar, nan ma lamarin bai canza ba domin a tattaunawar Aminiya da Malam Ibrahim Mai Bulo, ya tabbatar mata cewa kayan nasarufi dangin shinkafa, taliya, dawa da sauransu, sun fadi warwas.

A cewarsa, shinkafa ta dawo Naira dubu daya babban mudu maimakon Naira 1,800 da suke saya a makon da ya gabata yayin da taliya ta dawo Naira 250 maimakon Naira 400 a makon da ya gabata.

Canjin kudi ya yi mana daidai

A cewar malamin, “Mu wannan Canjin wasu kudaden Naira ya mana dai-dai.

“Kuma ai da ma watannin baya Baba Buhari ya ce mana, mu talakawa za mu samu saukin rayuwa nan gaba kadan, to a ganina ga shi nan mun fara gani kuwa.

“Fatanmu shi ne Allah Ya sa wannan kudiri na Baba Buhari na kawo sauki ga talakawa, Allah (SWT) ya dafa mana.

“Haka nan kuma Allah Ya yi rugu-rugu da duk wadanda za su motsa don kawo cikas a kai,” in ji shi.

Ya yi wannan batu ne ganin cewa karancin takardun kudi a hannun mutane ya sa jama’a cikin wani irin hali, amma ya ce komai mai wucewa ne in Allah Ya so.

An yi walkiya: Sauki ya zo —Mai Shago

A kan haka Malam Muhammad Nasiru Mai Shago cikin Babbar Tashar Motar Damaturu ya bayyana wa Aminiya cewa, “Ai wannan kunci ba komai ba ne illa alheri da zai faru gare mu, mu talakawa nan gaba.”

A cewar malamin, “Ai mun dau lokaci cikin ukubar da wasu mugayen ’yan kasuwa da ’yan bumburutun masu boye kayayyakin abinci suka jefa mu ciki.

“Amma sai ga shi a cikin makonni kalilan Allah (SWT) na shirin kawo mana sauki yayin da su kuma mugayen ’yan kasuwar ke kokawa dangane da wannan lamari, yayin da suka manta da halin da suka jefa mu a baya.

“Allah dai Ya saka wa Mai Girma Shugaban Kasa Baba Buhari dangane da wannan tsari da ya bullo da shi na canza fasalin wasu manyan takardun kudinmu na Naira.

“Don haka an yi walkiya mun gano na boye,” in ji shi.